IQNA

Taron Raya Daren Lailatul Qadr A Hubabaren Amirul Muminin

23:51 - June 04, 2018
Lambar Labari: 3482724
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne aka fara gudanar da tarukan raya daren lailatul qadr a hubbaren Imam Ali (AS) da ke Najaf.

 

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa masoya manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka ne suka taru a daren jiya domin raya daren lailatul qadr a hubbaren Imam Amirul muminin (AS) da ke Najaf Iraki.

A masallacin Imam Ali (AS) da ke birnin Kufah ma an gudanar da tarukan raya daren lailatul qadr tare da karatun addu’oi da salloli da suka kebanci wannan dare.

3720373

 

captcha