IQNA

Wani Matashi Bafalastnie Ya Yi Shahada

23:58 - June 06, 2018
Lambar Labari: 3482733
Bangaren kasa da kasa, Abdulhafiz Tamimi wan matashi bafalastine ya yi shahada bayan da sojojin yahudawa suka habe a kusa da Ramallah.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na haberler.com ya bayar da rahoton cewa, sojojin yahudawan sahyuniyan sun harbe matashin ne a garin Nabiyi Saleh da ke kusa da Ramallah.

Yahudawan sun harbe shi da harsashin bindiga ne a kansa, inda a nan take ya yi.

Majiyoyin ma’aikatar kiwon lafiya ta Palastine ta tabbatar da wannan labari a yau.

Tun bayan fara boren neman hakkokin palastinawa na komawa gida bayan tilasta su yin hijira fiye da shekaru hamsin da suka gabata, boren da aka fara cikin watanni biyu da suka gabata ya zu yanzu fiye da palastinawa dari da shirin ne suka yi shahada.

3720665

 

 

 

 

 

captcha