IQNA

Mutane Miliyan Biyu Sun Halarci Sallar daren Lailatul Qadr A Ka’abah

23:47 - June 12, 2018
Lambar Labari: 3482750
Bangaren kasa da kasa, fiye da mutane miliyan biyu nesuka halaci sallar daren 27 ga watan Ramadan da zimmar riskar daren lailatul qadr a Ka’abah.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya fiye da mutane miliyan biyu nesuka halaci sallar daren ashirin da bakawai ga watan Ramadan da zimmar riskar daren lailatul qadr a birnin masallacin harami mai alfarma.

Masu aikin Umrah daga sassan duniya ne suka cika masalacin harai mai alfarma na Ka’abah a daren na jiya domin samun falalar daren da wasu ‘yan sunna suke ganin yafi kusa da zama daren lailatul qadr.

Haka lamarin yakea  masallacin manzon Allah (ASW) a birnin Madina, inda a can dubban daruruwan masallata ne suka aru domin yin ibada a wannan dare.

A masallacin quds kuma duk da matakan da yahudawan Isra’ila suka dauka na kayyade adadin mutane masu shiga masallacin mai alfarma, fiye da mutane dubu 350 n suka gudanar da salar.

Yahudawan sahyuniya sun kayyade shekarun masallacin da cewa kada ska zama kasa da 40, amma duk da haka an cika masallacin makil.

3722196

 

 

 

 

 

captcha