IQNA

Taro Mai Taken Manzon Rahma A Uganda

23:05 - June 23, 2018
Lambar Labari: 3482781
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro mai take manzon rahma a kasar Uganda tare da halartar jami’an hukumar yada labarai ta UBC.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a  jiya ne gudanar da zaman taro mai take manzon rahma a kasar Uganda tare da halartar jami’an hukumar yada labarai ta kasar.

Babbar manufar taron dai ita ce yin bayani kan hakikanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa, wanda ya zo domin koyar da dan adam kyawan dabiu da kuma bin hakikanin tsarin rayuwa da yafi dacewa da shi.

Wannan taro dai yana samun karbuwa daga dukkanin bangarori na al’ummar kasar Uganda musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Kasar Uganda wadda mafi yawan mutanen kasar mabiya addinin kirista ne, amma kuma suna da kyakkyawar fahimtar juna da kuma zaman lafiya a tsakaninsu da musulmi.

3724518

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، amma ، kirista ، Uganda
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha