IQNA

Majalisar Malaman Addini Ta Aljeriya Ta Jinjina Wa Fatawar Ayatollah Khamenei

23:27 - June 26, 2018
Lambar Labari: 3482786
Bangaren kasa da kasa, babbar majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta jinjina wa fatawar Ayatollah Khamenei dangane wajabcin kare mutuncin matan manzon Allah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na TSA cewa, a zaman da ta gudanar jiya, babbar majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta jinjina wa fatawar Ayatollah Khamenei dangane wajabcin kare mutuncin matan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.

Majalisar malaman kasar ta Aljeriya ta bayyana wannan fatawa daga daya daga cikin manyan malaman mabiya mazhabar shi’ar ahlul bait (AS) na duniya da cewa, fatawa ce mai matukar muhimmanci, wadda ya zama wajibi dukkanin musulmi su yi aiki da ita.

Daga karshe majalisar ta yi jinjina da yabo maras misiltuwa ga jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Khamenei, tare da bayyana shi a matsayin malami mai son sulhu da hadin kan al’ummar musulmi.

3725416

 

 

 

 

 

 

captcha