Kamfanin dillancin labaran iqna, Usama Aufi babban mai shigar da kara na kasar bharain ya bayyana cewa, za a sake yin dubi dangane da hukuncin koton kasar, wanda ya wanke sheikh Ali Salamn dangane da zargin da ake yi masa na yi wa kasar Qatar aikin elekn asiri.
Ya ci gaba da cewa wannan mataki da kotun ta dauka ya saba wa kaida, domin wannan magana ce da ba za a taba bari ta wuce ba tare da kwakkwaran bincike ba.
Babban mai shigar da karar ya ce za a sake yin dubi a kan wannan zargi a ranar 5 ga watan satumba mai zuwa.
Tun a cikin shekara ta dubu biyu da sha hudu ce dai aka kama sheikh Ali Salman bisa dalilai na siyasa, amma daga bisani kuma aka zarge shi da yi wa kasar Qatar leken asiri, sakamakon tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da firayi ministan kasar Qatar ta wayar tarho kan halin da ake ciki da kuma kiran da suke yi na ganin an warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.