Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, shafin yada labarai na kare hakkin falastinawa da Isra'ila take tsare da ya sanar da cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen larabawa da wasu kasashen duniya sun bukaci Isra'ila ta saki Khalida Jarrar 'yar majalisar dokokin Palastine da ake tsare da ita tun shekarar da ta gabata.
Sharlut Kibs mai tuntuba na kunyar ya bayyana cewa, suna cikin tuntubar kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya kan batun tsare falastinawa ba bisa kaida da Isra'ila ke yi, kuma duk suna nuna shirinsu na tunkarar wannan zalunci.
Khalida Jarrar tana tsare ne tun a cikin watan Yunin shekarar da ta gabata, Isra'ila takame ta ne saboda nuna rashin amincewa da cin zarafin falastinawa da suke tsare a gidajen kason Isra'ila.