Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunne dangane da kokarin Amurka da wasu kawayenta na cimma wata yarjejeniyar da suka kira 'yarjejeniyar karni da nufin kawo karshen matsalar Palastinu don tabbatar da tsaron 'Isra'ila' yana mai bayyana cewar dakarun gwagwarmaya ba za su zuba ido ba.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a yammacin jiya Juma'a inda ya ce ya zama wajibi shugabanni da 'yan siyasar da suka damu da lamarin Palastinu su yi taka tsantsan da kuma daukar matakan da suka dace dangane da wannan makircin da Amurka da kawayenta da suka hada da wasu kasashen larabawa suke son kullawa.
A wani bangare na jawabin nasa, Sayyid Nasrallah ya bayyana cewa ko shakka babu dakarun sa kai na kasar Iraki da ake kira da Hashd al-Sha’abi za su mayar da martani ga harin da aka kai wa dakarun na su a lardin Dayr al-Zawr na kasar Siriya da yayi sanadiyyar shahada da kuma samun raunin wani adadi na dakarun.
Dangane da batun Yemen kuma shugaban kungiyar ta Hizbullah yayi watsi da labaran da suke cewa an kashe wasu 'yan kungiyar ta Hizbullah a kasar Yemen a lokacin da suka kai dauki ga dakarun Houthi na kasar Yemen din yana mai sake kiran Saudiyya da kawayenta da su kawo karshen kisan kiyashin da suke yi wa al'ummar Yemen din.
3726256
http://iqna.ir/fa/news/3726256