IQNA

23:53 - July 08, 2018
Lambar Labari: 3482816
Bangaren kasa da kasa, daruruwan yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun kutsa kai a yau a cikin masallacin quds mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau , daruruwan yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun kutsa kai a cikin masallacin quds mai alfarma tare da cikakkiyar kariya daga jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila.

Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan wani kutse da yahudawan suka yi a makon da ya gabata, inda suka shiga cikin harabar masallacin tare da keta alfarmarsa.

A yau ma yahudawan sun shiga har cikin ginin masallacin mai afarma, wanda hakan yana a matsayin wani mataki ne na tsokanar musulmi mazauan birnin.

Yahudawan Isra'ila dai sun jima suna aikata irin wannan danyen aiki, insda matasan palastinawa kan tare gabansu, amma a halin yanzu suna keta alfarmar masalalcin ne a hukumance tare da kariya daga gwamnatin yahudawa.

3728529

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: