IQNA

Kyauta Ta Musamman Ga Yara Masu Yin Sallar Asuba AMasallaci A Masar

0:00 - August 09, 2018
Lambar Labari: 3482875
Bangaren kasa da kasa, an ware kyautar wasu kudade da za a bayar ga yara wadanda suke yin sallar asuba a masallaci a lardin Buhaira na Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na bawwaba news cewa, a wani mataki na karfafa yara domin sallar asubahi, masallacin Damanhur ya ware kyautar wasu kudade da za a bayar ga yara wadanda suke yin sallar asuba a masallaci.

Bayanin y ace dukkanin yara da suka kai shekaru 10 zuwa 14 da suka yi salllar asuba sau 40 a cikin masallaci za a bas u kudi fan dubu daya wanda ya yi daidai da dalar Amurka 55.

Babbar manufar hakan dai ita ce karfafa gwaiwar yara da matasa kan lamarin salla.

Kasar Masar dai na daya daga cikin manyan kasashen musulmi da matasa ke bayar da himma wajen lamarin addini musamman kur’ani.

3736927

 

 

captcha