IQNA

23:41 - August 11, 2018
Lambar Labari: 3482883
Bangaren kasa da kasa, wani abin mamaki ya faru a cikin haramin Makkah inda wani maniyyaci ya yi yunkurin bude dakin ka'abah.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin tashar Russia today cewa, an nuna wani faifan bidiyoa  shafukan zumunta da ke dauke da wani abin mamaki da ya faru a cikin masallacin haramin Makkah inda wani maniyyaci ya yi yunkurin bude dakin ka'abah mai alfarma.

Mutumin dai ya iya tsallakawa zuwa bakin kofar dakin mai albarka, inda ya kama kyallen da da ke lullube da dakin Ka'abah, inda ya zame, wanda hakan yasa ya kasa bude kofar dakin.

Nan da nan jami'an tsaro sun kame mutumin, wanda ba a san dalilin da ya sanya shi yin wanna yunkuri ba, kuma sun tafi da shi wani wuri da ba a sani ba.

3737473

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bidiyo ، lullube ، dalili ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: