IQNA

23:55 - August 14, 2018
Lambar Labari: 3482893
Bangaren kasa da kasa, Wani malamin Ahlu sunnah dan kasar Saudiyay ya mutu a hannun jami'an tsaron kasar, sakamakon azbatrawar da suka yi masa.

kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, shafukan masu fafutuka da dama a kasa saudiyya sun nakalto cewa, Sheikh Sulaiman Al-Duwaish wanda tun ranar 22 ga watan Afirilun 2016 jami'an tsaro suka saka shi cikin daurin Talala, ya fuskanci azabtarwa mai tsanani a hannun jami'an tsaro, inda a jiya aka samu labarin mutuwarsa.

Bayan nada Muhammad Bin Salman dan gidan sarkin Saudiyya a matsayin yarima mai jiran gado, ya kame mutane da dama ya wurga su gidan kaso, da suka hada da malamai, da lauyoyi gami da masu fafutukar kare hakkokin bil adama da sauransu, sakamakon sukar salon siyasarsa da suke yi.

3738560

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: