IQNA

23:40 - August 19, 2018
Lambar Labari: 3482905
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin kare hakkokin 'yan kasa a kasar Qatar ya sanar da cewa,a shekarar bana Saudiyya ta haramta wa maniyyata daga kasar ta Qatar zuwa aikin hajji domin sauke farali.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abdullah Ka'abi, daya daga cikin mambobin kwamitin kare hakkokin 'yan kasa a Qatar ya tabbatar mata da cewa, gwamnatin kasar ta Saudiyya ta dauki wasu kwararan matakai a kan maniyyata na kasar Qatar, da hakan ya haramta musu zuwa aikin hajjin bana.

Ya ce daga cikin matakan kuwa, har da toshe safin yanar gizo da Saudiyya ta bude domin bayar da visa ga maniyyata daga kasar Qatar, wanda babu wata hanya da za su iya karbar izinin shiga kasar ta wannan hanyar.

3739585

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، qatar ، hajjin bana ، saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: