IQNA

0:00 - August 23, 2018
Lambar Labari: 3482916
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron masarautar Saudiyya sun awon gaba da Sheikh Saleh Al Talib daya daga cikin limaman masallacin haramin Makka mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna; Jaridar Qods Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron sun kame Sheikh Saleh ne bayan da ya yi gargadi kan bayyana munanan ayyuka na sabon Allah.

Rahoton ya kara da cewa malamin ya aike da wasika a asirce zuwa ga kwamitin walwalwar 'yan kasa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya kafa, inda ya yi kakkausar suka ayyukan da kwamitin yake gudanarwa, musamman abubuwan da suka shafi aikata badala a fili a cikin kasar.

Malaman addini da dama ne  gami da masu rajin kare hakkokin 'yan adam har da ';yan gidan sarautar kasar ta Saudiyya ne Muhammad Bin Salman ya jefa su kurkuku, sakamakon sukar salon siyasarsa a kasar.

3739950

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Saudiyya ، Makka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: