IQNA

23:56 - August 24, 2018
Lambar Labari: 3482922
Bangaren majalisar dinkin duniya ta yi kakkausar suka dangane da irin halin da musulmin Rihingya suke ciki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi, ya bayyana cewa, Antonio Guterres na cikin damuwa matuka kan halion da muuslmi 'yan kabilar Rohingya suke ciki a Mayanmar.

Ya ce babban abin takaici ne irin halin da aka bar wadannan mutane a ciki, da kuma yadda aka yi musu cin zarafi da raba su da kaddarorinsu da kuma tilasta dubban daruruwa daga cikinsu yin hijira.

Ya ce babau wani hanzari da mahukuntan Myanmar za su bayar. Dole ne su dauki matakin kare rayukan wadannan mutane, kuma a tabbatar da an shirya mayar da wadanda suka yi gudun hijira zuwa yankunasu.

3740788

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: