Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar addinin musulunci ta Azhar a kasar Masar ta bayyana cewa, irin matakan da Isra'ila take dauka na murkushe Falastinawa masu bore a yankin jabal Raisan da ke gabashin Ramallah ya saba wa dukkanin dokoki na duniya.
Bayanin ya ce nauyi ne da ya rataya kan al'ummomin kasashen duniya da su takawa Isra'ila burki kan cin zarafin al'ummar Palastine da take yi.
A cikin wannan makon ne Isra'ila ta fara kaddamar da wani aikin gina sabbin matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa da ke Jabal Raisan a gabashin birnin Ramallah, inda dubban matasan Falastinawa suka fito domin nuna rashin amincewa da hakan, amma sojoji da jami'an 'yan sanda Isra'ila suna ci gaba da murkushe su da karfin bindiga.