IQNA

Taron Makokin Shahadar Imam Sajjad (AS) A Moscow

23:56 - October 04, 2018
Lambar Labari: 3483026
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron makokin shahadar Imam Sajjad (AS) a birnin Moscow na kasar Rasha.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da taron makokin shahadar Imam Sajjad (AS) a birnin Moscow na kasar Rasha a ranar Asaba mai zwa.

Kwamitin masalacin khatamul anbiya ne y dauki nauyin shirya wannan taro, wanda zai samu halartar Hojjatol Islam Saber Akbari wakilin wilayatol faqih a Mosco, da kuma wasu daga cikin malamai.

Za a gabatar da jawabai a wurin dangane da matsayin Imam Sajjad, da kuma iin darussan da suke a cikin rayuwarsa mai albarka.

A ranar 25 bisa wasu ruwayoyi Imam Sajjad ya yi shahada, wanda kuma mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suna gudanar da tarukan tunawa d shahadarsa.

3752748

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، morocco ، rasha ، Imam Sajjad
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :