IQNA

Mutane Dubu 7 Ne Suka Sanya Kansu Aikin Bayar Da Agajin Gaggawa A Arbaeen

23:44 - October 23, 2018
1
Lambar Labari: 3483068
Bangaren kasa da kasa, cibiyar bayar da agajin gaggawa ta Helal Ahmar a kasar Iraki ta sanar da cewa mutane dubu 7 ne suka shiga cikin masu bayar da agajin gaggawa a ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bisa ga bayanin da cibiyar bayar da agajin gaggawa ta Helal Ahmar a kasar Iraki ta bayar, ta tabbatar da cewa mutane dubu 7 ne suka sanya kansu bayar da agajin gaggawa a ziyarar arbaeen a Krbala.

Baynain y ace baya ga wadannan mutanen, wasu 1500 kuma sun sadaukar da kansu domin kwashe shara da datti a lokacin gudanar da ziyarar arbaeen.

Sadeq Hussaini shugaban kwamitin tabbatar da tsaro na lardin Dayali ya bayyana cewa, mayakan sa kai na Hashd Sha’abi sun shiga gudanar da ayyukan bayar da kari ga masu ziyarar arbaeen.

Ya ce mayakan na Hashd suna kan dukkanin tituna da suke isa birnin karbala, inda suke yin aiki kafada da kafada tare da jami’an tsaro.

3758390

 Mutane Dubu 7 Ne Suka Sanya Kansu Aikin Bayar Da Agajin Gaggawa A Arbaeen

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
idris
0
0
Ina farin chiki da murnar zagayowar ranar yaumul arbauna Allah yasa a gama lafiya labbaika ya Hussein as
captcha