IQNA

23:57 - October 29, 2018
Lambar Labari: 3483081
Bangaren kasa da kasa, an fara rijistar sunayen wadanda suke da sha’awar shiga gasar kur’ani mai tsarki da ta kebanci nakasassu a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yaum Sabi cewa, yanzu haka an fara rijistar sunayen masu son shiga gasar kur’ani mai tsarki da ta kebanci nakasassu wadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar take daukar nauyin shiryawa.

A wannan shekara sharadin shiga gasar dai shi ne shekarun mai son shiga gasar kada su haura 25, haka nan kuma ya zama ko dai ya hardace kur’ani baki daya, ko kuma ya hardace rabi, ko izihi goma sha biyar, tare da sanin ka’idojin karatu.

Ga masu sha’awar shiga gasar dai kofa bude take domin yin rijista daga nan har zuwa kwanaki goma sha biyar.

Daga karshen gasar kuma za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a gasar.

3759327

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: