IQNA

Sarkin Gargajiya A Uganda Ya Bukaci Kara Bunkasa Alaka Da Iran

23:56 - November 04, 2018
Lambar Labari: 3483099
Bangaren kasa da kasa, sarkin gargajiya a kasar Uganda ya bukaci da akara bunkasa alaka da kasar Iran a dukkanin bangarori.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Uganda Muhammad Ridha Qazlesfali a lokacin da yake ganawa da sarkin gargajiya na kasar Uganda Kassim Nakibinge Kakungulu a fadarsa da ke yankin Kibulu a cikin birnin kampala fadar mulkin kasar Uganda, ya bukaci da a kara bunkasa alaka da kasar ta Iran da kuma Uganda.

Sarkin y ace yay aba matuka da irin rawar da iran take takawa musamman a kasashen gabashin Afrika, inda take bude makarantu da cibiyoyin addini, tare da taimaka ma musulmi da ma wadanda ba muuslmi ba, wanda hakan ya kara fito da kyakkyawar fuskar addinin musulunci ga al’ummomin wadannan yankuna.

Haka nan kuma ya kara da cewa, kasantuwarsa musulmi yana alfahari da irin gagarumin ci gaban da musulmi suke samu a kasar Uganda, da kuma yadda suke zaune lafiya tare da ‘yan uwansu mabiya sauran addinai, musamman ma kiristoci wadanda su ne suke da rinjaye a kasar.

A kan ya ce kara bunkasa alaka da Iran musamman a bangarori na ilimin kimiyya da fasaha zai taimaka matuka ga kasar, maimakon dogaro da turawa a kowane lokaci.

3761045

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، uganda ، iran ، Kampala
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha