IQNA

20:39 - November 09, 2018
Lambar Labari: 3483115
Bangaren kasa da kaa, majami'oin mabiya addinin kirista a kasar Amurka sun nuna rashin amincewa da shirin da Isra'ila take da shin a kwace kaddarorin majami'o a Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Russia yaum ta bayar da rahoton cewa, majami'u da dama ne a cikin kasar Amurka suka aike da wasi zuwa ga sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Mike Pompeo, inda suke bukatar da a dakatar da Isra'ila dangane da shirinta na kwace kwaddarorin majami'u a birnin Quds.

Bayanin ya ce, majami'un sun tabbatar wa Pompeo da cewa ba za su taba amincewa da yunkurin Isra'ila na gabatar da wani kudiri ga majalisar Knesset domin amincewa da kwace kaddarorin mabiya addinin kirista ba.

A ranar Lahadi mai zuwa ce dai gwamnatin Isra'ila za ta gabatar da wani daftarin kudiri a gaban majalisar Knesset, da ke nufin samun amincewar majalisar domin kwace kaddarorin mallakin majami'un kiristoci.

Kimanin kashi 28 na yankin kasa da ke Quds malakin majami'un kiristoci, da suka hada da coci-coci, kasuwanni, makarantu da asibitoci da otel-otel da filaye, wanda Isra'ila ta ce za ta kwace su baki daya, saboda ba a biya musu haraji.

3762336

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: