IQNA

23:53 - November 28, 2018
Lambar Labari: 3483158
Bangaren kasa da kasa, jam’iyyar Green Party a kasar Jamus ta bukaci da a amince da addinin mulsunci a hukumance a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ne aka bude babban taron musulmi na kasar Jamus, a birnin Berlin fadar mulkin kasar, tare da halartar Horst Seehoferministan harkokin cikin gida na kasar ta Jamus.

A yayin gudanar da zaman taron ne ‘yan jam’iyyar Green Party suka bayyana cewa suna kokarin ganin an amince da addinin mulsunci a kasar a hukumance, kamar yadda aka amince da sauran addinai da kungiyoyi masu dauke da akidu daban-daban a kasar.

Katrin Göring-Eckardt shugabar gungun ‘yan majalisar dokokin Jamus na jam’iyyar Green Party ta bayyana a wurin taron cewa, sun gabatar da daftarin kuduri a majalisar dokokin kasar ta Jamus, da ke neman a amince da addinin muslucnia  kasar a hukuamnce.

Amincewa da musuluncia  a hukuamnce a Jamus zai baiwa muuslmi damar gudanar da addininsu a cikin ‘yanci a hukuamnce, kamar yadda kuma za su rika gudanar da bukukuwansu na addini da kuma ba su hutu a wuraren ayyukansu.

3768001

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: