IQNA

Gwamnatin Hollanda Ta Dakatar Da Sayarwa Saudiyya Da Makamai

19:48 - November 30, 2018
Lambar Labari: 3483166
Gwamnatin kasar Holland ta dakatar da sayar wa Saudiyya da ma kasashen da suke cikin kawance da Saudiyya ke jagoranta, da ke kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, minista mai kula da harkokin kasuwanci da kasashen ketare a Holland Sigrid Kaag ta sanar a gaban majalisar dokokin kasar cewa, sun dakatar da sayar wa Saudiyya da makamai, da sauran kasashen da suke cikin kawance da ke kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar Yemen karkashin jagorancin kasar ta Saudiyya.

Ta ci gaba da cewa, wannan mataki zai hada da kasashen Masar da kuma UAE, sakamakon rawar da suke takawa wajen taimaka ma Saudiyya a hare-haren da take kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen.

A kwanakin baya ne majalisar kungiyar tarayyar turai ta bukaci dukkanin kasashen da suke cikin kungiyar, da su dakatar da sayarwa Saudiyya da makamai, sakamakon kisan Jamal Khashoggi da kuma yakin da take kaddamarwa kan al'ummar Yemen.

3768201

captcha