Kamfanin dillancin labaran iqna, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki bugun China a babban baje kolin littafai na hukumar raya al’adu da tarihi ta majaliosar dinkin duniya UNESCO da ke gudana a halin yanzu a birnin Paris na kasar Faransa.
Wannan baje koli dai ya hada da littafai na tarihi da kuma wadanda aka rubuta su domin raya wasu harsuna ko al’adu na wasu al’ummo a duniya, kamar yadda aka nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarkia wurin.
Kwafin kur’anin da yafi daukar hnkali shi ne wanda aka buga a China, wanda kawata shi da rubutu kuma aka dora shi a kan dardumar Farisa wadda ake sakawa a kasar Iran.
Ana gudanar da baje kolin ne akowace shekara, a shekaru masu za a gudanar da shi a kasashen Austria, Jamus, Turkiya, Spain, Birtaniya da kuma Amurka.