IQNA

Tawagogin Yamen Sun Cimma Matsaya Kan Abubuwa 4 A Sweden

23:59 - December 13, 2018
Lambar Labari: 3483214
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kwamitin koli na juyin juya halin kasar Yemen ne ya bayyana haka a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter a yau alhamis

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kwamitin ya kuma jinjinawa manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya akan kasar Yemen, Martin Friffiths saboda kwazon da ya nuna a tattaunawar sulhun da take gudana a kasar Sweeden

Sai dai al-Huthy ya jaddada wajabcin cimma matsaya akan bude filayen jiragen sama na Aden da Siyun domin hakan zai kara karfafa hadin kan kasar Yemen da hana ta darewa.

Al-Huthy ya ce a halin yanzu wadannan filayen jiragen saman suna a hannun 'yan mamaya ne, don haka  wajibi ne ga Majalisar Dinkin Duniya da ta yi abin da za ta iya domin warware wannan batu

A gefe daya shugaban tawagar Ansarullah a tattaunawar da ake yi a kasar Sweeden Muhammad Abdussalam ya jaddada ya ce al'ummar Yemen ba za su taba laminta a ci gaba da zaman sojojin kasashen waje a cikin kasarsu ba.

A yau alhamis ne ake sa ran cewa babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutrres zai halarci tattaunawar, domin karfafa bangarorin Yamen su kara fahimtar juna da warware sabanin da yake tsakaninsu.

 

3772124

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha