IQNA

Sabbin 'Yan Majalisar Dokokin Amurka Musulmi Za Su Yi Rantsuwa Da Kur'ani

21:18 - December 21, 2018
Lambar Labari: 3483239
Bangaren kasa da kasa, sabbin 'yan majalisar dokokin Amurka biyu wadandanda dukkaninsu mata ne kuma musulmi, sun ce za su yi rantsuwa da kur'ani mai tsarki a gaban majalisar dokokin kasar ta Amurka.

Sabbin 'Yan Majalisar Dokokin Amurka Musulmi Za Su Yi Rantsuwa Da Kur'aniKamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Free Press ya bayar da rahoton cewa, Rashida Tlaib daya daga cikin mata musulmi da suka samu nasarar lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka ta bayyana cewa, za ta tafi da kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen turanci domin rantsewa da shi.

ta ce za ta tafi tare da Ilhan Umar wadda daya ce daga cikin muusmi mata da suka lashe zaben na 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka, inda za su yi rantsuwar tare.

Tlaib ta ce za ta tafi da kwafin kur'anin da George Sale ya tarjama a shekara ta 1732 ne, domin tabbatar wa Amurkawa da cewa kur'ani ba bakon littafi ne a kasar Amurka ba.

Shekaru 12 da suka gabata ma Keith Ellison wani dan majalisar dokokin Amurka musulmi, yayi rantsuwa da kur'ani mai tsarki, inda wasu daga cikin Amurka suka yi ta yin suka kan hakan, tare da bayyana cewa kur'ani bakon littafi da ba  asan da zaman shi a  kasar Amurka ba.

3774292

 

 

 

 

captcha