IQNA

Hamas Ta Yi Watsi Da Shawarar Amurka Kan Yadda Za A Kafa Kasar Palastine

23:25 - December 24, 2018
Lambar Labari: 3483247
Kungiyar gwagwarmar Falastinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Amurka ta gabatar kan yadda za a kafa kasar Palastine, inda hakan zai takaita ne kawai da yankin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da ya yi da kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri, ya tabbatar da cewa ba za su taba amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar ba a matsayin hanyar sulhu da Isra'ila, inda take ganin cewa a kafa gwamnatin Palastine amma yankin Gaza kawai.

Ya ce wannan shawara ce wadda babu wani bafalastine mai kishi da zai taba amincewa da ita, domin kuwa Palastine ba zirin Gaza ce kawai, domin kuwa Gaza shi ne yanki mafi kankanta a cikin Palastine da ke karkashin mamayar Isra'ila, kuma birnin Quds shi ne babban birnin Palastine ba Gaza ba.

A kan haka ya ce duk wata magana wadda ba ta ginu a kan mayar wa falastinawa da yankunansu da Isra'ila ta mamaye ba, Hamas ba za ta taba amincewa da ita ba.

Wannan shiri na Amurka dai yana daga cikin shirin da ake kira yarjejeniyar karni, wadda Amurka da Isra'ila gami da Saudiyya da Jordan da kuma Masar suka shirya, kuma suke da nufin aiwatar da ita.

3774670

 

captcha