Kamfanin dillancin labaran iqna, dakarun na kasar Masar sun kddamar da wannan harin ne da jijjifin safiyar yau, biyo bayan harin da aka kai jiya akan wata motar bas da take dauke da wasu 'yan yawon bude 'yan kasashen ketare, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu.
Ma'ikatar harkokin cikin kasar Masar ta ce a jiya Juma'a 'yan ta'addan sun kai hari kan motar bas din wadda take dauke da 'yan kasar Viatnam su sha hudu inda uku daga cikinsu gami da wani dan kasar Masar mai yi musu tafinta suka rasa rayuansu, sauran kuma suka samu munanan raunuka.
Har yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai harin bam din, amma dai tuni mahukuntan kasar ta Masar suka dora alhakin hakana kan 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyah takfiriyya da suke da alaka da alkaida, wadanda suke kai hare-hare kan jama'a da sunan jihadi.