IQNA

Malaman Addini Sun Goyi Bayan Hana Caca A Kasar Uganda

20:00 - January 31, 2019
Lambar Labari: 3483340
Bangaren kasa da kasa, malaman addinai na muslunci da kristanci a kasar Uganda sun goyi bayan matakin hana caca  akasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, David Bhati ministan harkokin tattalin arziki na kasar Uganda ya bayyana cewa, bisa umarnin shugaban kasar Yuweri Museveni, an hana bayar da lasisi ga ‘yan caca a kasar.

Ya ci gaba da cewa, malaman addini na muslunci da kiristanci a kasar Uganda sun goyi bayan matakin hana caca a kasar saboda illar da take da ita  cikin al’umma.

Ministan ya kara da cewa, caca tana da babbar illa ta take ahifarawa ga harkokin tattalin arzikin kasa, domin kuwa kamfanonin caca suna zuwa kasar suna karbar kudaden mutane sun afita da su, wanda hakan a cewarsa yana da babban tasiri ga tattalin arzikin kasar.

A nasu bangaren malaman addinai na kirista da muuslmia  kasar sun ce caca ta sabawa koyarwar wadannan addinai guda biyu, saboda haka suna goyon bayan matakin na gwamnati.

3785906

 

captcha