IQNA

21:44 - February 10, 2019
Lambar Labari: 3483359
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron tunawa da zagayowar cikar shekaru 40 na samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a dakin taron DUSIT THANI da ke birnin Manila na kasar Philipines.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da taron tunawa da zagayowar cikar shekaru 40 na samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a kasar Philipines tare da halartar masana da malamai da ‘yan siyasa gami da baki ‘yan kasashen ketare.

Wannan taro wanda ya hada da jami’an diflomasiyya na kasashe daban-daban, ya yi dubi kan cikar shekaru 40 na samun nasarar juyin muslucni a Iran da kuma tasirinsa a cikin wadannan shekaru.

Baya ga jami’an diflomasiyya dam asana da kuma malaman addinin muslucni gami da Iraniyawa mazauana kasar, wasu daga mabiya addinin kirista sun halarci wurin.

Babbar manufar taron wanda ofishin jakadancin Iran a kasar Philipines ya dauki nauyin shiryawa, ita ce kara fito da matsayin kasar ta Iran kan abubuwa da sua shafi siyasar duniya, da kuma yadda kasar take gain wajabcin tabbatar da adalci a tsakanin al’ummmin duniya.

Haka nan kuma Iran tana ganin cewa lokaci ya yi day a kamata kasashen duniya su zama masu ‘yanci na hakika  dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki, maimakon ci gaba da zama bayi ko ‘yan amshin shata ga kasashe ‘yan mulkin mallaka masu girman kai.

3789026

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: