IQNA

16:59 - February 12, 2019
Lambar Labari: 3483365
Bangaren kasa da kasa, Ilhan Umar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta yi kakkausar suka kan salon siyasar zaunci ta Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ilhan Umar ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta yi kakkausar suka kan salon siyasar zaunci ta Isra’ila a kan al’ummar Palastine.

A cikin wani bayani da ta rubuta a shafinta na twitter Ihan ta bayyana cewa, bai kamata kasa kamar Amrka mai bin tafarkin dimukradiyya ta zama mai kare siyasar zalunci da kama karya ba.

Ta ce tsarin salon mulkin Isra’ila ba na dimukradiyya ba, tsari ne na danniya da nuna wariya ga wasu marassa karfi, saboda haka bata goyon bayan ci gaba bayar da kariya ga irin wannan tsari.

Wannan bayani na Ilhan ya jaw tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin jami’an Amurka, inda wasu ke ganin cewa, hakan zai iya kawo bababr Baraka da gibi a dangantakar Amurka da Isra’ila.

3789231

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، Ilhan Umar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: