IQNA

23:41 - February 22, 2019
Lambar Labari: 3483395
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Isra’ila sun kame Falastinawa a yankuna daban-daban da ke kusa da birnin Quds a yau.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labaran arabi 21 cewa, a yau , jami’an tsaron Isra’ila sun kame Falastinawa a yankuna daban-daban da ke kusa da birnin Quds da nufin ganin sun hana Falastinawa gudanar da gangami a cikin birnin da kewaye.

Wannan mataki dai yana zuwa nebayan kiran da dukkanin kungiyoyin Falastinawa suka yi ga dukkanin mutanen Quds da sauran yankuna da ke gabar yamma da kogin Jordan na cewa su hadu a birnin Quds a ranar Juma’a domin buyde kofar masallacin mai alfar ta babu rahma, wadda jami’an tsaron Isra’ila suka kulle ta.

An zuba daruruwan jami’an tsaron yahudawa a cikin da wajen harabar masallacin mai alfarma, amma duk da haka dubban Falastinawa daga ciki da wajenbirnin Quds sun hallara a masallacin, kuma sun bude kofar babu rahma a gaban jami’an tsaron Isra’ila.

A yankin zirin Gaza kuwa yahudawan sun kasha wani matashi bafalastine tare da jikkata wasu dadama.

3792276

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Gaza ، isra’ila ، quds
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: