IQNA

23:50 - March 09, 2019
Lambar Labari: 3483438
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da bude cibiyoyin hardar kur’ani guda 70 a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai Al-sabah ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da bude cibiyoyin hardar kur’ani guda 70 a fadin kasar kuma yanzu haka mutane 4441 sun yi rijistar sunayensu a cibiyoyin.

Bayanin ya kara da cewa, mafi yawan wadanda suka yi rijistar sunayensua  wadannan cibiyoyi dai mata ne, kuma ana sa ran adadin zai ci gaba da karuwa a cikin ‘yan lokuta masu zuwa.

Haka nan kuma yanzu haka ana shirin bude wasu cibiyoyin a biranan Akahira, Sinai ta arewa, Iskandariyya, Diqhaliyya da Suiz.

3796530

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Alkahira ، Masar ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: