IQNA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadiyar Kenya A Tehran

23:41 - March 18, 2019
Lambar Labari: 3483468
Ma'ikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadiyar kasar Kenya a Tehran, domin nuna rashin jin dadi kan hukuncin da wata kotun Kenya ta fitar ci gaba da tsare wasu Iraniyawa biyua kasar ta Kenya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran bahram Qasemi ya bayyana cewa, an kirayi jakadiyar kasar ta Kenya a Tenran Rukayyah Subo, domin nuna rashin gamsuwa da hukuncin da wata kotun kasar Kenya yanke da ke yin watsi da batun sakin wasu Iraniyawa biyu da ake tsare da su a kasar.

Ya ci gaba da cewa, ma'ikatar harkokin waje ta mika dukkanin sakon da ya dace ga jakadiyyar ta kasar Kenya a Tehran, domin mika shi ga mahukuntan kasar Kenya.

A cikin Fabrairun 2018 ce dai kotun kolin kasar Kenya ta wanke Iraniyawan biyu daga dukkanin tuhumce-tuhumcen da 'yan sanda Kenya ke yi a kansu, tare da bayar da umarnin sakinsu, amma jami'an tsaro sun ci gaba da rike.

Qasemi ya ce hukuncin da wannan kotu ta yanke ya yi hannun riga da hukuncin babbar kotun kolin kasar ta Kenya.

3798650

 

captcha