Kafofin yada labaran Palastine sun bayar da rahoton cewa wani matashi bafalastine ya yi shahada a Bait laham.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, shafin yada labarai na Albayan News ya bayar da rahoton cewa, sakamakon bude wutar bindiga da sojojin Isra’ila suka yi a kan wasu Falastinawa a kusa da matsugunnin yahudawa na Dahisha, matasa da dama sun samu raunuka.
Wannan matashi mai suna Sajid Muzhim dan shekaru 17 da haihuwa ya yi shahada ne sakamakon raunukan day a samua jiya.
Rahoton ya kara da cewa, Falastina da dama sun samu raunkuna sakamakon harehatren, inda yanzu haka wasu ke kwancea asibiti ana kula da su.