IQNA

22:29 - April 04, 2019
Lambar Labari: 3483517
Gwamnatocin kasashen Iran da Iraki sun soke kudaden karbar izinin shiga kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Furat News na kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, bangaren kula da lamurran 'yan kasashen ketare a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ya sanar da cewa, daga ranar Litinin da ta gabata, kasar ta janye karbar kudade daga hannun Iraniyawa masu karbar takardun izinin shiga cikin kasar ta Iraki.

I\bayanin ya ce wannan na cikin dokar kundin tsarin mulkin kasar Iraki mai lamba 76, da aka amince da ita a cikin 2017, wadda ta tanadi cewa, duk kasar da ta janye karbar kudaden visa daga Irakawa, to gwamnatin Iraki ma za ta janye karbar kudaden visa daga mutanen wannan kasar.

A ranar ta Linin ce dai ofishin jakadancin Iran da ke birnin bagadaza na kasar Iraki ya sanar da jaye karbar kudaden visa daga dukkanin Irakawa masu shiga cikin kasar ta Iran, wanda a ranar ne ita Iraki da fitar da sanarwa makamnciyar wannan.

3800649

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: