IQNA

Martanin Majalisar Dokokin Iran Ga Amurka Kan Batun IRGC

23:48 - April 17, 2019
Lambar Labari: 3483553
Yan majalisar dokokin Iran sun kada kuri’u mafi rinjaye na amincewa da daftarin dokar da aka gabatar na mayar da martani akan matakin da Amurka ta dauka akan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran IRGC.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ‘Yan majalisa 204 ne daga jimillar ‘yan majalisa 256 suka amince da bayyana rundunar tsakiya ta sojojin Amurka da Santicom da dukkanin bangarorin da suke karkashinta a matsayin ‘yan ta’adda. Bugu da kari kudurin ya kuma bayyana cewa duk wani taimakon da za a iya wa wannan rundunarna kudi, ko na bayanan sirri ko kayan aiki, daidai yake da taimakawa ayyukan ta’addanci.

Har ila yau, kudurin ya kira yi gwmanatin jamhuriyar musulunci ta Iran da ta dauki matakan da take ganin sun dace wajen fuskantar ayyukan ta’addancin Amurka da suke a matsayin barazana ga manufofin jamhuriyar musulunci ta Iran.

A makon da ya shude ne dai Amurka ta bakin shugaban kasar Donad Trump ta bayyana dakarun kare juyin musulunci na Iran a matsayin ‘yan ta’adda.

 

3804375

 

 

 

 

captcha