IQNA

23:26 - April 27, 2019
Lambar Labari: 3483584
Kwamitin kare hakkokin addinai da mabiyansu na kasar Amurka, ya yi Alawadai da kisan da masarautar saudiyya ta yi wa masu adawar siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kwamitin ya fitar a jiya, ya kirayi gwamnatin Amurka da ta dakatar da dukkanin matakan da take dauka na mara baya ido rufe a kan kisan ‘yan adawar siyasa a kasar Saudiyya bisa tuhumce-tuhumce marassa tushe.

Bayanin ya kara da cewa, kisan ‘yan shi’a fiye da talatin da gwamnatin Saudiyya ta yi batu ne na siyasa da bangaranci da kuma tsorata masu adawa da tsarin mulkiyya a kasar.

Kwatin ya ce yin gum da baki da gwamnatin Amurka take a  kan irin wanann ta’asa, zai kara tabbatar wa duniya da cewa da masaniyarta komai ke gudana, amma saboda maslaharta ta yi shiru da bakinta.

A ranar Talatar ad ta gabata ce dai masarautar saudiyya ta sare kawunan mutane ralatin da bakawai, talatin daga cikinsu ‘yan shi’a ne da ta kame, bisa laifin shiga gangamin nuna adawa da salon mulkin kama karya a kasar, inda aka kashe su bisa tuhuma ta ta’addanci.

3806658

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: