IQNA

23:49 - April 28, 2019
Lambar Labari: 3483586
Bangaen kasa da kasam cibiyar tattara bayanai kan halin da Falastinawa suke ciki ta Wadil Hulwa ta sanar da cewa, yahudawa sun yi kame falastinawa 40.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na Ma’a ya bayar da rahoton cewa, a yau Lahadi cibiyar tattara bayanai kan halin da Falastinawa suke ciki ta Wadil Hulwa ta sanar da cewa, yahudawan sahyuniya  sun yi kame falastinawa 40 a yakin Al’isawi da ke gabashin birnin Quds sun yi awon gaba da su.

Bayanin ya kara da cewa, jami’an tsaron gwamnatin yahudawan sun tafi da dukkanin Falastinawan da suka kame zuwa ofishins da ke yankin Maskubiya a cikin birnin Quds.

A ranar Asabar da ta gabata ma jami’an tsaron yahudawan sun kame wani karamin yaro  mai suna Mu’utaz Abdullah da shekarunsa ba su wuce goma ba.

3807189

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، karamin yaro ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: