Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin arab News cewa, Jam’an alasiri babban jami’in hulda da jama’a a na kwamitin kula da masallacin ma’aiki ya sheda cewa, za su dauki nauyin buda bakin mutane rabin miliyan a daren karshe na watan Ramadan.
Ya yanzu yanzu haka sun kammala dukkanin shirin da ya kamata domin wannan babban taron buda baki.
Haka nan kuma ya kara da cewa, mutane dubu 5 a ka dauka domin yin aiki a wurin, kama daga tsaftace wurin da kuma shirya shi da raba abinci.
Ya kara da cewa kafin lokacin buda bakin dai za a gudanar da karatun kur’ani mai tsarki inda za a sauke kur’ani kafin lokacin faduwar rana.