IQNA

23:51 - July 10, 2019
Lambar Labari: 3483827
Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka wadda ta samu goron gayyata daga masarautar Saudiyya domin halartar taron rawa a Jidda ta janye shirinta na halartar taron.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, Tashar Arab  News ta bayar da rahoton cewa, a  cikin wani bayani da ta fitar, Nicki Minaj ta bayyana cewa ta janye halartar taron rawar ne da za a gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiyya, domin kare hakkokin mata da kuam masu auren jinsi.

Kafin lokacin dai wasu rahotanni daga kasar ta Saudiyya sun tabbatar da cewa, sakamakon yadda jama’a da dama musamamn masu kishin addini daga cikin mutanen kasar, sun nuna rashin jin dadinsu da wannan mataki, wanda hakan yasa ala tilas mahukuntan na Saudiyya suka janye gayyatar da suka yi mata.

Nicki Minaj wadda shaharriyar mawakiya ce ‘yar kasar Amurka, ta gudanar da wakokinta a cikin taro tare da sanya tufafi masu fitar da tsiraici, kuma yariman mai jiran gadon sarautar kasar ta Saudiyya Muhammad Bin Salman ne da kansa ya gayyace ta zuwa taron wakokin da za a gudanara  Jidda a mako mai zuwa.

Ko a watan da ya gabata, Maria Keri tare da wasu fitattun mawaka mata Amurka sun halarci taron wakokin na Jidda, duk kuwa da nuan rashin amincewa da jama’a da dama a kasar suka nuna.

 

 

3826035

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، saudiyya ، Nicki Minaj
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: