IQNA

23:44 - July 11, 2019
1
Lambar Labari: 3483828
shugaba Rouhani na kasar Iran ya ce jamhoriyar musulinci ta Iran za ta ci gaba da barin kofofin Diflomasiya da tattaunawarta a bude.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yayin da yake ganawa da mai bawa shugaban kasar Faransa shawara kan harakokin siyasa Emmanuel Bonne jiya laraba a birnin Tehran, Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayana fatansa game da sabon yunkurin Shugaba Macron na Faransa inda ya ce ya kamata bangarorin biyu su yi amfani da wannan dama wajen cimma manufofin da suka sanya a gaba na tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015.

Shugaba Rouhani ya kara da cewa manufar jamhoriyar musulinci ta Iran shi ne dukkanin alkwarikan da bangarorin biyu suka dauka suka cika su ta yadda za a zartar da dukkanin yarjejjeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015, ita ma kasar Iran za ta dakatar da kudirin da ta dauka na ci gaba da tace sinadirin karfen Uranium a nan gaba.

A yayin ganawarsa da Shugaba Rouhani mai bawa shugaban kasar Faransa shawara kan harakokin siyasa Emmanuel Bonne ya mika masa sakon da ya zo da shi na shugaba Emanuel Macron.

A yayin da ya kai ziyarar birnin Tehran Emmanuel Bonne ya gana tare da tattaunawa da Ministan harakokin wajen Iran Muhamad Jawad Zarif da kuma babban saktaren Majalisar Tsaron Kasa Ali Shamkhani.

3826214

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rauhani ، Iran
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
tarishin manzon allah (saw)
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: