IQNA

21:57 - July 16, 2019
Lambar Labari: 3483847
Dan takarar neman kujerar Firaim ministan kasar Britania ya bayyana kiyayyarsa ga addinin musulunci a wata hira da ta hada shi da jiridar Guardina ta kasar Britania.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar ta Guardian ce ta bayyana haka a jiya Litinin, inda ta nakalto Boris Jonson yana fadar cewa addinin musulunci, addinin koma baya ne ga ga al-ummar duniya.

Amma kamfanin Tell MAMA wanda yake aikin lissafa mizanin kiyayyar da musulmim suke fuskanta a kasar Britania, ya bayyana cewa maganganun na Boris Jonson sun nuna cewa ya jahilci addinin musulunci.

Banda haka wasu rahotannin sun bayyana cewa kashi 52% na yan majalisar dokokin kasar Britania sun jahilcin matsayin da addinin musulunci ya ke da shi a tarihin bil’adama.

Kafin furucinsa na bayan bayan nan dai, Boris Jonson ya taba sifanta mata musulmi masu sanya hajibi a matsayin barayin banki.

Masana suna ganin da alamun idan Jonson ya haye kan kujerar Firai ministan kasar Biritania, yana iya kara takurawa musulman kasar.

3827562

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Birtaniya ، Johnson
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: