IQNA

23:50 - July 17, 2019
Lambar Labari: 3483849
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Kenya sun nuna damuwa kan matakan da jami'an hukumar kula da fice ta kasar ke dauka kansu a lokacin hajji.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, majalisar musulmin kasar Kenya ta fitar da bayani, wanda a cikinsa take yin korafi kan irin matakan da jami'an hukumar kula da shige ta kasar take dauka a kan muuslmia  duk lokacin aikin hajji.

Bayanin majalisar musulmin kasar ta Kenya ya ce, ana samun matsaloli a bangaren karbar fasfo a kasar a lokacin da musulmi suke tafiya hajji, inda ake wahalar da su matuka.

Majalisar ta ce tana yin Allawadai da hakan, tare da kiran mahukunta da su dauki matakin bin kadun wannan lamari cikin gaggawa, domin gano masu hannu a ciki domin taka musu birki, domin hakan yana a matsayin nuna wariya da banbanci ga musulmi ne.

Kasar Kenya da ke gabashin Afrika, na daga cikin kasashen da musulunci ya fara zuwa tun a cikin karni na uku na hijira kamariyya, kuma yawan muuslmin kasar ya kai kashi 15 cikin dari.

3827979

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Kenya ، hajji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: