IQNA

23:54 - July 17, 2019
Lambar Labari: 3483851
Jami’i mai wakiltar tarayyar Afirka a tattaunawa tsakanin fararen hula da sojojin Sudan ya bayyana cewa ya gana da wakilin sojoji na Sudan a kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, Wakilin na tarayyar Afirka ya kara da cewa; An tsara yin taron ne a jiya Lahadi, amma an dage shi bisa bukatar masu wakiltar fararen hula.

Wata majiyar daga Sudan ta ce an kuma sami sabani a tsakanin bangarorin biyu dangane da bai wa sojojin da za su kasance cikin gwmanatin rikon kwarya, rigar kariya.

A shekaran jiya Asabar dubban mutanen kasar ta Sudan ne su ka fito kan titunan biranen kasar domin tunawa da cikar kwanaki 40 da kashe masu zaman dirshan da sojoji kasar su ka yi.

Kungiyoyin kasa da kasa sun yi tir da abin da ya faru a wancan lokacin, tare da yin kira da a hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a kashe fararen hular masu Zanga-zangar lumana.

A cikin watan Aprilu ne dai al’ummar kasar ta Sudan su ka kifar da gwamnatin shugaba Umar Hassan al-Bashir wanda ya shekara 30 yan akan karagar mulki.

 

3827879

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، sojoji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: