IQNA

23:54 - July 18, 2019
Lambar Labari: 3483853
Bangaren siyasa, ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Iran za ta yi tsayin daka a kan yakin tattalin arzikin da aka kaddamar a kanta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jamhuriyar musulinci ta Iran, ta sake yin allawadai, da takunkunman ta’addancin tattalin arzikin da Amurka ta kakaba mata, domin cimma haramtatun manufofinta na siyasa.

Da yake bayyana hakan, yayin wani taro kan ci gaba mai daurewa, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Muhammad Jawwad zarif, ya ce, al’ummar kasarsa, na fama da wani yanayi na ta’addanci mai tsauri kan tattalin arziki, wanda ya shafi wadanda basu san hawa basu sauka ba, kawai domin cimma wasu haramtattun manufofin siyasa.

Zarif ya kara da cewa, wadannan takunkuman, da ‘’basa bisa doka’’ sun kawo cikas sosai ga jamhuriya musulinci ta Iran, wanda kuma hakan yake zaman babban cikas ga kokarin da Iran din take na samar da ci gaba mai daurewa, hatta ma ga kasashe makobtanta.

A watan Mayu, na shekara dubu biyu da sha takwas ne gwamnatin Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran, kan shirinta na nukiliya, sannan daga bisani ta fara yi wa Iran ruwan takunkuman ba kakkautawa, wanda kuma hakan ya nakasa tattalin arzikin kasar.

Amurka dai na zargin Iran, da kokarin mallakar makamin nukiliya, da kuma dagula al’amura a yankin gabas ta tsakiya, zargin da Iran ke ci gaba da musantawa.

A mtsayin maida martini kan takunkuman Amurka, Iran ta fara wani shiri na dakatar da aiki da wasu daga cikin bangarorin da yarjejeniyar da aka cimma da ita, ciki har da tatse sinadarin uranium son ranta

3828051

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Zarif ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: