IQNA

23:56 - July 19, 2019
Lambar Labari: 3483858
Bangaren kasa da kasa, Mark Lowcock babban jami’in majalisar dinkin duniya kan harkokin agaji ya caccaki Saudiyya da UAE kan batun Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babban jami’in majalisar dinkin duniya kan harkokin agaji Mark Lowcock ya yi kakkausar suka a kan kasar Saudiyya, dangane da kunnen uwar shegu da take yi da dukkanin kiraye-kirayen da ake yi mata kan batun yakin Yemen.

Jami’in na majalisar dinkin duniya ya yi ishara da cewa, sakamakon yakin na Yemen, da kuma asarori da ya jawo wa miliyoyin mutanen kasar, Saudiyya da UAE sun yi alkawalin cewa za su bayar da dala miliyan 750 domin taimaka ma wadanada yakin ya tagayyara, amma ko dala daya ba su bayar ba.

A cikin shekaru fiye da hudu da Saudiyya ta kwashe tana kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen, ya zuwa yanzu dubban fararen hula ne suka rasa rayukansu sakamakon wadannan hare-hare, tare da rusa dubban gidajen jama’a, da daruruwan masallatai, da daruruwan cibiyoyin kiwoyan lafiya da makarantu gami da kasuwanni da sauransu.

 

3828219

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: