IQNA

22:57 - July 28, 2019
Lambar Labari: 3483890
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da janazar shugaban kasar Tunisia tare da halartar shugabannin kasashen duniya.

kamfanin dillancin labaran iqna, a, kasar Tunisia a jiya Asabar ne akayi jana’izar shugaban kasar Béji Caïd Essebsi, wanda Allah, ya yi wa rasuwa a ranar Alhamis data gabata, yana mai shekaru 92 a duniya.

Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar, har da shugaban kasar faransa, Emanuel Macron, da shugaban Palasdinawa Mahmud Abass, da shugaban gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya Faez Al’Saraj, da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani.

An dai yi jana’izar ce tare da halatar iyalen mirigayin, da girmamawa ta sojoji gaban dimbin al’ummar kasar ta Tunisia.

Mirigayi Béji Caïd Essebsi dan ashekaru 93 a duniya, shi ne wani shugaban kasa na farko a Tunisia da aka zaba ta hanyar demokuradiyya, bayan guguwar neman sauyi da ta kawo karshen tsohuwar gwamnati.

3830286

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: