IQNA

23:01 - July 31, 2019
2
Lambar Labari: 3483898
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan hare-haren Saudiyya a Saada.

Kamfanin dillacin labaran iqna, shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da MDD kan kisan fararen hular da Saudiyya ta yi a garin Saada, bayanin majalisar ya yi kakkausar suka kan wannan danyen aiki.

Lise Grande babbar jami’ar majalisar dinkin duniya a bangaren ayyukan agaji akasar emen ta bayyana cewa, hakika hare-haren da Saudiyya ta kaddamar a ranar Talata da ta gabata kan wata kasuwa  a garin Sa’ada da ke arewacin Yemen aiki ne da ya cancanci tir da Allaawadai.

Bayanin ya ci gaba da cewa, harin na Saudyya yay i sanadiyyar mutuwar fararen hula 14 da jikkatar wasu da dama daga ciki kuwa har da kananan yara.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a duniya sun dora alhakin wannan kisan gilla a kan gwamnatin Amurka, sakamakon goyon bayan da take baiwa Saudiyya kan kisan farare hula a Yemen, da kuma sayar mata da makaman da ke kai hare-haren da su.

 

3831583

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Yemen ، Saudiyya
Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
MUHD INUWA ISAH
0
0
ALLAH YEWADARAN NAKA YALALA CE WAIYANZU SAUDIYA ITACE TAZAMA ABINDA AMAIRIKA TAKE AMFANI DASHI WAJAN KASHE MUSILMAI
IDRI YAKUBU MUHD
0
0
Gaskiya yakamata saudiyya ta gyara halayanta, kuda xa'ai koyi daku.
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: