IQNA

23:59 - August 19, 2019
Lambar Labari: 3483967
Bangaren siyasa, albarkacin zagayowar lokacin idin Ghadir jagora ya yi wa fursunoni afuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a  yau Litinin ne jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayar da umarni a saki fursunoni da adadinsu ya kai 1070 saboda bukukuwan babbar salla da kuma Ghadir.

Umarnin da jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, ya biyo bayan shawarar da shugaban ma’aikatar shari’a ta kasar Hajjatul Islam wal musulimina Ra’isy ya gabatar ne na yi wa wasu fursunonin afuwa.

Dama dai wani kwamiti na musamman ya kammala tantance wadanda yin afuwar za shafa.

A gobe ne ake bikin ranar Ghadir wacee manzon Allah ( S.A.W) ya ayyana Imam Ali ( A.S) a matsayin jagoran al’ummar musulmi bayansa.

3836038

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: